Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sanarwar gyara yawan mazauna birnin Wuhan da suka mutu sakamakon cutar COVID-19
2020-04-17 11:36:26        cri
Yau ofishin dake jagorantar ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar COVID-19 na birnin Wuhan da ke kasar Sin ya ba da wata sanarwa cewa, ya zuwa karfe 12 na daren ranar 8 ga watan Afrilu, yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu da 325 a birnin bayan da aka sake yin kididdiga, lamarin da ya sa yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai 50333 gaba daya. Yayin da yawan mazauna birnin da suka mutu sakamakon cutar ya karu da 1290 bisa adadin da aka bayar a baya, hakan ya sa an gyara yawan matattu sakamakon cutar har zuwa 3869 a birnin.

Sanarwar ta ce, an samu wadannan sabbin alkaluma ne bayan da kungiyar bincike kan alkaluman da suka shafi annobar da ilmin cututtuka masu yaduwa wadda ke karkashin jagorancin ofishin ba da umurni kan aikin dakile yaduwar cutar COVID-19 ta birnin Wuhan, ta hada kai tare da hukumomin da suka shafi kiwon lafiya, yaki da cututtuka, tsaron jama'a, harkokin jama'a, shari'a, kididdiga na birnin, wajen sake tattara bayanan dukkan wadanda suka kamu da cutar daga tsare-tsaren intanet na tattara bayanai yadda aka dakile yaduwar cutar, bayanan matattu, bayanan masu kamuwa da cutar a asibitoci, da bayanan sakamakon binciken lafiyar mutane na birnin, baya ga sake tattara bayanan daga wuraren da suka shafi annobar, kamar sassan kula da masu zazzabi, asibitocin yau da kullum, asibitocin wucin gadi, wuraren killacewa, unguwanni masu ganon wadanda ke kamuwa da cutar, da gidajen kurkuku da hukumomin kula da tsoffi na gwamnati. Sa'an nan kuma an sake yin kididdiga bisa taimakon hukumomin jinya, unguwanni, ofisoshin 'yan sanda, wuraren aikin wadannan mutane da ma iyalansu.

Haka kuma sanarwar ta nuna cewa, an yi hakan ne bisa "Dokar kandagarki da shawo kan cuttuttuka masu yaduwa ta Sin", da "Ka'idojin tinkarar lamuran kiwon lafiyar jama'ar ba zata", da "Ka'idojin gudanar da ayyukan kididdiga na Sin", da "Ka'idojin tafiyar da harkokin yin rajista kan bayanan matattu na kasar", kuma bisa aniyar mutunta tarihi, da al'umma, da ma matattu.

Sanarwar ta ce, dalilan da suka sa alkaluman suka sha bamban da na baya shi ne sabo da, na farko an samu yawan masu kamuwa da cutar da sauri sosai a farkon bollar cutar a Wuhan, lamarin da ya haddasa karancin kayayyakin jinya, da gazawar karbar masu kamuwa da cutar, inda wasu suka mutu a gida kafin su je asibiti. Na biyu, a lokacin da ake kokarin ceton mutane masu yawan gaske, asibitoci sun gudanar da ayyukan jinya fiye da kima, har ma ba a iya sanar da bayanan masu dauke da cutar da wadanda suka mutu a kan lokaci. Na uku, wasu hukumomin jinya ba su shiga tsare-tsaren tattara bayanai na intanet a kan lokaci ba, sakamakon saurin karuwar yawan asibitocin da ake kwantar da wadanda ke dauke da cutar, kamar asibitocin da ke karkashin ma'aikatar lafiyar kasar Sin, da na lardi, da na birni, da na unguwanni, da na masana'antu, da masu zaman kansu, da na wucin gadi da dai sauransu. Na karshe kuma shi ne sabo da ba a yi rajistar wasu bayanan matattun yadda ya kamata ba, lamarin ya haddasa gabatar da kuskuren bayanan da suka shafi masu dauke da cutar.

Daga karshe, sanarwar ta ce, rayuka na da muhimmanci, haka ma jama'a. Duk wanda ya mutu sanadiyyar annobar abu ne mai matukar bakin ciki ga iyalinsa, da kuma birnin. Don haka, muna nuna jaje ga iyalan wadanda suka mutu sakamakon cutar COVID-19, da ma nuna ta'aziyyar 'yan uwanmu da suka riga mu gidan gaskiya da ma'aikatan jinya da suka sadaukar da rayukansu yayin yaki da annobar.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China