Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya zanta da Putin game da yaki da COVID-19
2020-04-17 10:57:17        cri
A daren jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Vladimir Putin. Yayin zantawar ta su shugaba Xi ya sake jaddada cikakken goyon bayan kasar sa, a yakin da duniya ke yi da cutar numfashi ta COVID-19, yana mai watsi da matakan siyasantar da batun cutar.

Shugaba Xi ya ce yayin da wannan cuta ke bazuwa a sassan duniya, kasashe na fama da aiki mai wahalar gaske na yaki da ita. Ya kuma yi waiwaye game da tattaunawa ta wayar tarho da ya yi tare da shugaba Putin kusan wata guda da ya gabata, inda a wancan lokacin ma suka yi musayan ra'ayi, tare da bayyana matsaya, game da hanyoyi mafiya dacewa na yin hadin gwiwa, wajen kandagarki da kuma shawo kan wannan cuta.

Shugaba Xi ya ce hakan ya sake jaddada karfin dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Ya ce siyasantar da batun wannan annoba ta COVID-19, na iya illata hadin gwiwar kasa da kasa a wannan fanni. Kaza lika shugaban ya ba da shawarar ci gaba da aiki tare, tsakanin Sin da Rasha, a wani mataki na samar da tsaro, da inganta harkokin kiwon lafiyar duniya.

A nasa bangare kuwa, shugaba Putin cewa ya yi, yunkurin wasu mutane na bata sunan kasar Sin, ta hanyar alakanta kasar da zama tushen cutar COVID-19 ba abu ne da za a amince da shi ba.

Ya ce Rasha a shirye take ta kara karfafa musaya, da hadin gwiwa da kasar Sin a sassa daban daban, cikin hadda ayyukan dakile yaduwar cutar, da inganta tattaunawa, da hadin gwiwa a wadannan fannoni tare da MDD. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China