Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mazauna birnin Wuhan na farin cikin sake bude garinsu
2020-04-08 15:18:39        cri

Da karfe 12 na daren jiya Talata ne, aka kawar da dukkan matakan hana shigi da fici da aka sanya a birnin Wuhan da ke kasar Sin. Daga lokacin hunturu zuwa lokacin bazara, wannan birnin na farfadowa sannu a hankali. A hannu guda kuma mazauna birnin na farin ciki matuka da sake bude garin nasu.

Mr. Xia, wani mazauni birnin ya yi murnar cewa, "Na dade ban fita waje ba, yanzu na ji kamar yawon bude ido nake yi. Ko da yaushe ina da imanin cewa, hakika za mu samu nasara a kan cutar COVID-19, ga shi yanzu mun iya. Al'amura za su kyautata sannu a hankali a Wuhan."Mr. Xia ya bayyana cewa, bayan an bude birnin, abu mai muhimmanci dake gabansa shi ne saduwa da iyalai da ma abokai.

Birnin Wuhan ya fara tafiyar da harkokinsa, kuma ma'aikata sun fara komawa bakin aiki. A game da shiri na gaba, Mr. Wu, jami'in wani kamfani ya bayyana cewa, abin da ya fi tunawa shi ne yadda za a gabatar da bukatar dawowa bakin aiki.

Killace birnin Wuhan da sauran wurare ya sa mazauna birnin sun kara kaunar sa. Madam Chen ta furta cewa, "Abin da ya sha bamban da na baya shi ne, yanzu birnin Wuhan ya warke, kuma ya dawo kamar yadda yake a da. Ina fatan jama'a za su ci gaba da kaunar Wuhan."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China