Sin ta tura tawagogin likitoci zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sanar a yau Alhamis cewa, gwamnatin kasar Sin ta tura tawagogin masu aikin likitanci na yaki da cutar numfashi ta COVID-19, zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso. Kwamitin kiwon lafiyar kasar Sin ya kafa wadannan tawagogi biyu, wadanda masu aikin likitanci, da kwamitin kiwon lafiyar lardin Sichuan, da kwamitin kiwon lafiyar birnin Tianjin suka zaba. Kuma tawagogin biyu sun tashi daga nan kasar Sin a yau Alhamis. (Maryam)
Labarai masu Nasaba