Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya ce kasarsa za ta tallafawa Sudan a yaki da COVID-19
2020-04-17 10:42:15        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa al'ummar Sinawa a shiye suke su yi aiki tare da jama'ar Sudan, a yakin da suke da annobar COVID-19, kuma gwamnatin Sin za ta tallafa musu gwargwadon karfinta.

Ya bayyana hakan ne a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho tare da firaministan Sudan Abdalla Hamdok. Ya ce jama'ar kasar Sin a shirye suke su yi aiki tare da jama'ar Sudan, tare da ba su goyon baya da taimako gwargwadon hali, domin yakar annobar ta COVID-19.

Li ya kara da cewa, annobar abokiyar gabar bil adama ce kuma babu wata kasa a duniya da zata iya yakar cutar a kashin kanta, ya kara da cewa, alummar Sinawa a shirye suke su yi aiki tare da sauran al'ummar kasa da kasa ciki har da mutanen Afrika, domin kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta, domin samun lafiya ga jama'ar duniya baki daya.

A nasa bangaren, Hamdok yace bangaren Sudan yayi matukar nuna godiya bisa ga taimakon da kasar Sin ke baiwa kasa da kasa wajen yaki da annobar COVID-19, kuma ya kalubalanci duk wani mataki na nuna wariya da wasu kasashe ke aikatawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China