Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Wuhan ya fitar da sabon shirin maido da zirga-zirga
2020-04-08 13:26:47        cri

Daga yau Laraba 8 ga wata, an fara bude hanyoyin fita daga birnin Wuhan da lardin Hubei da ke kasar Sin. Domin tabbatar da ganin harkokin zirga-zirga sun gudana yadda ya kamata, birnin Wuhan ya fitar da sabon shirin maido da zirga-zirga, inda aka bayyana cewa, za a bude hanyoyin bisa shirin da aka tsara yadda ya kamata, baya ga daukar matakai da suka dace don tabbatar da komai ya tafi lami lafiya.

Wadannan matakai sun hada da bukatar fasinjoji da za su shiga motar bas, su nuna manhajan dake tabbatar da lafiyarsu da ke wayoyin salulansu. Sa'an nan an jibge ma'aikata a motocin bas, da jiragen kasa da ke karkashin kasa, da jiragen fito, da manyan motoci masu yin dogon zango, domin tabbatar da fasinjoji sun sanya marufin hanci da baki da nuna manhajan dake tabbatar da lafiyarsu, da auna zafin jikinsu, da kiyaye oda yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, an kara yawan sa'o'in fesa maganin kwayoyin cuta a tashoshin mota da na jiragen kasa.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China