Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci a ba kasashen Afrika cikakkiyar damar warware matsalolin nahiyar
2019-10-08 10:29:20        cri
Wakilin kasar Sin ya bayyana muhimmancin baiwa kasashen Afrika cikakkiyar damar warware matsalolin da suka shafi nahiyar Afrikan.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce kamata ya yi a ba da cikakken goyon baya ga Afrika, kuma a samu cikakken yakini kan manufofin da kasashen suka bullo da su, wadanda za su taimaka wajen warware matsalolin da suka shafe su.

Ya ce kamata ya yi a yi amfani da matakan riga kafin tashe tashen hankula ta hanyar mutunta dokokin dake shafar ikon mulkin kasashen.

Zhang ya kuma bayyana muhimmancin dake tattare da irin rawar da kungiyoyin shiyyar zasu taka misali kamar kungiyar tarayyar Afrika.

Ya ce ya kamata kasashen duniya su taimakawa Afrika wajen cimma muradun cigaba nahiyar ta hanyar aiwatar da matakai na zahiri.

Kasar Sin a shirye take ta hada shawarar ziri daya da hanya daya tare da ajandar kungiyar AU ta bunkasa Afrika nan da shekarar 2063, da ajandar samar da dawwamamman cigaba ta MDD nan da shekarar 2030, da kuma sauran dabarun bunkasa cigaban kasashen Afrika, da ingiza hanyoyin cigaban kasashen, da samar da dawwamamman zaman lafiya ta hanyar bunkasa cigaba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China