Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An jinjinawa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika duk da kalubale da ake fuskanta
2019-09-10 10:24:58        cri

Wasu wakilai da suka gabatar da jawabai yayin wani taron rabin yini, game da hadin gwiwa da cudanyar dake wanzuwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a sassa daban daban, sun jinjinawa wannan alaka da suka ce ta haifar da da mai ido.

Mahalarta taron da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a jiya Litinin, sun ce karkashin hadin gwiwar sassan biyu, Sin ta tabbatarwa duniya cewa, ita sahihiyar abokiyar hulda ce ga kasashen Afirka.

Da yake tsokaci yayin taron, shugaban kwamitin wakilan dindindin na kungiyar tarayyar Afirka ta AU Osman Abdel Khalek, ya ce baki dayan nahiyar Afirka na amfana daga hadin gwiwarta da Sin, musamman duba da cewa Sin ta riga ta shata sassan hadin gwiwar ta, gwargwadon bangarorin da Afirka ke baiwa muhimmanci, da ma bangarorin da daidaikun kasashen nahiyar ke baiwa fifiko.

A nasa tsokaci kuwa, jakadan kasar Sin a kungiyar AU Liu Yuxi, ya jaddada cewa, a halin yanzu duniya tana fuskantar wani irin sauyi da ba a tsammata ba, wanda hakan ya sa Sin da kasashen Afirka, ci gaba da rungumar kudurorin ci gaba tare.

Ya ce, "za mu karfafa cudanya, da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, kana za mu kara azama wajen daidaita tsare-tsaren ci gaba, ta yadda za a kai ga cimma nasarori a zahiri, irin wadanda za su amfani karin mutane, su kuma haifar da makoma mai haske ga hadin gwiwar Sin da Afirka.

An dai shirya taron na karawa juna sani ne karkashin hadin gwiwar ofishin wakilcin Sin a AU, da cibiyar bincike, da musayar yawu da hadin gwiwa ta CDRC, karkashin taken "Wanzar da kawance na gargajiya,". Taron ya kuma mai da hankali ga fayyace irin nasarori da aka samu, da ma inda aka dosa, karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China