Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da tallafawa Afirka duk da batun takaddamar cinikayya tsakaninta da Amurka
2019-07-23 15:53:14        cri

Jakadan Sin a kasar Namibia Zhang Yiming, ya ce a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki, Sin za ta ci gaba da tallafawa kasashen nahiyar Afirka, da goyon bayan cudanyar cinikayya tsakanin sassa daban daban, duk kuwa da takaddamar cinikayya dake wakana tsakaninta da Amurka.

Jakadan na wannan tsokaci ne yayin taro game da albarkatun ruwa da ke gudana tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Windhoek, fadar mulkin Namibia.

Jakada Zhang ya ce Sin na da babbar kasuwa, da yawan masu sayayyar hajoji, don haka tana maraba da kawayenta na Afirka ciki hadda Namibia, da su rika shigar da nasu hajoji cikin kasuwannin Sin.

Ya ce "Ina tabbatar muku cewa kofar Sin a bude take ga hada hadar shige da fice daga Afirka, kuma za mu ci gaba da bude kofofinmu ga abokanmu ciki hadda na kasashen nahiyar Afirka". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China