Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tashar kan tudu ta Sin ta samu bunkasar harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare
2020-04-14 10:52:35        cri

Babbar tashar jigilar kayayyaki ta jirgin kasa ta Alataw Pass dake jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin, ta samu bunkasar harkokin jigilar kayyayakin da aka saya ta intanet zuwa ketare.

A rubu'i na farko na bana, an yi jigilar kunshin kayayyakin da aka saya ta intanet 287,400 da darajarsu ta kai dala 520,000 daga tashar zuwa kasashen Turai, ciki har da Belgium da Jamus.

A ranar 21 ga watan Junairu ne tashar Alataw Pass ta kaddamar da kasuwanci ta intanet tsakanin kasa da kasa, inda take fitar da kayayyakin wasa da na katako da sutura da sauran abubuwan bukatun yau da kullum.

Kunshin kayayyakin da aka fitar ta jirgin kasa na daukar rabin lokacin da za a dauka idan aka tura ta ruwa. Yayin da ake fuskantar wannan annoba, kudin jigilar kayayyakin ya kai kasa da kusan kaso 70 bisa dari idan aka kwatanta da na jirgin sama.

An yi kiyasin a bana, za a yi jigilar kunshin kayayyaki miliyan 20 zuwa kasashen Turai ta tashar Alataw Pass. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China