Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na daukar dukkanin baki mazauna kasar a matsayi daya
2020-04-09 20:48:48        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce aikin gaggawa dake gaban kasar a halin yanzu, game da yaki da cutar COVID-19 shi ne dakile shigo da cutar daga waje, da hana sake bullar ta a cikin gida.

Mr. Zhao ya yi wannan tsokacin ne, yayin taron manema labarai na rana rana da ya gudana a Alhamis din nan. Yana mai cewa, cimma nasarar hakan ya danganta da irin fahimta, da tallafi, da kuma hadin gwiwar dukkanin Sinawa da baki mazauna kasar. Kaza lika gwamnatin Sin na daukar dukkanin baki 'yan kasashen waje dake zaune a cikin kasar Sin a matsayi daya, tana kuma adawa da duk wani mataki na nuna banbanci, ko dai ta hanyar furka wasu kalamai, ko aikata wani hali na nuna kyama.

Rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai dai sun yi ikirarin cewa, ana nunawa wasu 'yan Afirka mazauna lardin Guangdong da ma wasu sassa na kasar ta Sin kyama, lamarin da ke da nasaba da yunkurin dakilewa ko shawo kan cutar COVID-19.

Da yake amsa tambaya game da hakan, Zhao Lijian ya ce tun barkewar cutar covid-19, Sin da kasashen Afirka na ci gaba da goyawa juna baya, suna kuma hadin gwiwa wajen yaki da wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China