Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Annobar COVID-19 ka iya dadewa
2020-04-11 20:11:44        cri
Zhong Nanshan, shehu malami, kuma kwararren likita na kasar Sin, ya yi musayar ra'ayi da wasu kwararru na kasar Koriya ta Kudu, ta kafar intanet bisa gayyatar da aka yi masa a jiya Juma'a. Inda shehun malamin ya ce, ba zai yiwu a samu kawar da cutar COVID-19 baki daya a duniya ba, don haka watakila cutar za ta dade tana yaduwa a kasashe daban daban. A cewar masanin, ya kamata a yi kokarin neman samun allurar rigakafin cutar, maimakon a bar mutane su kamu da ita, sa'an nan wasu daga cikinsu da suka warke daga cutar za su iya samun rigakafin cutar da kansu. A ganin mista Zhong, matakin barin mutane su kamu da ita, zai kai ga asarar rayuka da dama.

A ganin Zhong, yanayin yaduwar cutar COVID-19 a duniya ya shafi bangarori 2. Na farko shi ne halayyar cutar, inda ya ce, yanzu kananan kwayoyin halittu na Gene dake cikin kwayar cutar COVID-19 sun riga sun canza tsarinsu, inda suka sanya kwayar cutar ta saba da muhallin dake cikin jikin dan Adam, da samun yaduwa cikin sauri matuka. Sa'an nan karfin kisa na cutar ya ninka na mura har sau 20. Sai dai bisa la'akari da al'adar kwayoyin cuta, yaduwar cututtukan tsarin numfashi kan yi sauki a lokacin zafi.

Batu na biyu da zai tabbatar da yanayin yaduwar cutar COVID-19 shi ne matakan da aka dauka na shawo kanta. A cewar shehun malamin na kasar Sin, saboda cutar tana kisa matuka, ya kamata a gagauta ayyukan nazari don samar da allurar rigakafin cutar, maimakon a bar galibin mutane su kamu da ita, don su samu rigakafin cutar da kansu. Masanin ya ce, hakan ba zai yiwu ba, don zai salwantar da rayuka masu dimbin yawa. Sa'an nan, ya kamata a mayar da hankali ga matakin nisantar juna, domin ya kasance wani muhimmin mataki da za a iya dauka na magance yaduwar cutar tsakanin mutane.

Masanin ya kara da cewa, yanzu haka masana ilimin halittu na kasar Sin na kokarin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19. Sai dai ana bukatar yin wannan allura kan dubu-dubatar mutane, don haka dole a lura sosai. A cewar mista Zhong, a kan dauki shekara daya zuwa biyu kafin a samar da allurar rigakafin wata cuta. Duk da cewa zai yiwu a kara saurin aikin, la'akari da tsananin bukatar dake akwai. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China