Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka na iya cimma nasara ne kawai idan sun hada kai wuri guda
2020-04-08 21:11:49        cri
Kusan Amurkawa masu fada a ji 100 ne suka fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, wadda ke kira ga Amurka da Sin, da su hada karfi waje guda a aikin kandagarkin annobar da duniya ke fuskanta.

Da yake tsokaci game da hakan a ranar Talatar nan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce ra'ayin mutanen ya yi daidai da gaskiya, ya kuma dace da kiraye-kiraye da al'ummun kasashen biyu, da ma sassan kasa da kasa ke ta yi cikin 'yan kwanakin nan, wanda kuma ya samu karbuwa ga kasar Sin.

Jami'in ya sake nanata hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana ta kafar bidiyo a dai ranar ta Talata, yana mai cewa cutar numfashi ta COVID-19 da ake fama da ita a duniya ba ta da wani shinge, kuma kalubale ce ga daukacin al'ummar duniya. Don haka Sin a shirye take ta shiga a dama da ita, wajen tabbatar da nasarar kafuwar al'ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin al'ummu. Za ta kuma ci gaba da aiki tare da Amurka, da sauran kasashen duniya wajen karfafa hadin gwiwar samar da kariya, ga lafiyar al'ummar duniya baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China