Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhao Lijian: Kalaman Mike Pompeo ba su da tushe bare makama
2020-04-09 20:47:33        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi watsi da kalaman sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, game da zargin boye hakikanin halin da Sin ta shiga game da barkewar cutar COVID-19.

Da yake kore kalaman na Mr. Pompeo, Mr. Zhao Lijian ya ce Sin ce ta fara gabatar da rahoton barkewar cutar COVID-19 ga hukumar WHO, amma hakan ba ya nuna cewa, birnin Wuhan na kasar Sin ne cibiyar cutar. Ya ce batun wai Sin ta boye yaduwar cutar ba shi da tushe ko makama.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokacin ne, yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa game da wannan batu, yana mai cewa cuta na iya barkewa a ko wane yanki ko wuri dake wata kasa ko shiyya a duniya, amma gano hakikanin cibiyar cutar batu ne da masana kimiyya, da kwararru a fannin kiwon lafiya kadai ke iya tabbatarwa.

Zhao ya kara da cewa, kamata ya yi dukkanin kasashe su sanya batun kare rayukan al'umma, da kiwon lafiyar su gaban komai. Kuma abu ne a zahiri, cewa karkashin jagorancin JKS, Sin ta cimma manyan nasarori a fagen yaki da wannan annoba. Don haka shafa kashin kaji, da dora laifi kan wani, ba zai taimaka wajen kawar da cutar ba.

Daga nan sai ya yi fatan cewa, Amurkawa su ma za su kai ga shawo kan wannan annoba cikin gaggawa. Kaza lika za su yi watsi da halin rashin dattaku na wasu 'yan siyasar kasar, wadanda ke kokarin siyasantar da batun cutar, suna kyamatar kasar Sin, tare da kokarin kautar da tunanin al'umma daga gaskiya, suna dorawa wasu laifi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China