Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Za a kara sanar da gano wadanda ke dauke da cutar COVID-19 ba tare da nuna alamu ba
2020-04-08 10:41:14        cri

Hukumar kiwon lafiyar kasar Sin, ta wallafa a shafinta na Intanet cewa, a dare jiya 7 ga wata, an kira taro ta kafar bidiyo da waya domin nazari kan yadda za a gudanar da ayyukan dakile yaduwar cutar COVID-19 bayan da an bude hanyoyin zirga-zirga daga birnin Wuhan da ma lardin Hubei zuwa sauran wurare. Inda Ma Xiaowei, shugaban kwamitin ya jaddada cewa, yadda aka bude hanyoyin shigi da fici na birnin Wuhan bayan da aka rufe shi har na tsawon kwanaki 76 ya alamta yadda aka samu babban ci gaba wajen takaita yaduwar cutar a kasar Sin, amma lamarin ya haifar da sabon kalubale ga aikin dakile yaduwar cutar a kasar.

Mr. Ma ya kuma bayyana cewa, bude birnin ba ya nufin babu bukatar rigakafi. Babu sabon mai kamuwa da cutar kuma ba ya nufin babu hadari ko kadan. Maido da zirga-zirga ba ya nufin an amince kowa zai iya fita waje ba tare da yin tunanin komai ba. Ya kamata wurare daban daban na Sin su kara dora muhimmanci kan aikin sanar da gano wadanda ke dauke da cutar ba tare da nuna alamu ba. Sa'an nan a lura da sabbin masu kamuwa da cutar, da wadanda ke bukatar tantacewa kan kamuwa da cutar, da ma masu dauke da cutar ba tare da nuna alamu ba, domin a kara yin bincike game da cutar mai yaduwa.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China