Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gidauniyar Jack Ma ta kaddamar da gasar gwarazan matasa 'yan kasuwa ta Afrika
2020-04-08 14:10:01        cri

Gidauniyar Jack Ma ta kaddamar da gasar gwarazan matasa 'yan kasuwa ta Afrika kashi na 2, domin bada kyautuka ga 'yan kasuwa masu tasowa dake bada gudunmuwa cikin al'ummominsu.

'Yan kasuwa daga kasashen Afrika 54 daga dukkan fannonin rayuwa da kasuwanci za su samu damar neman shiga gasar da za a bada kyautar dala miliyan 1.5 ga mutane 10 da suka yi nasara.

Mutanen 10 za kuma su samu damar shiga shirin dake karfafa gwiwar matasa 'yan kasuwa ta Africa Netpreneur Prize Initiative, don samun dabaru da horo da kwarewar da ake bukata wajen samun nasara a kasuwanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China