Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taimakawa kasashen Afrika 18 da kayayyakin kiwon lafiya na yaki da COVID-19
2020-04-07 14:41:49        cri
Kayayyakin kiwon lafiya na yaki da COVID-19 da kasar Sin ta bayar ga kasashen Afrika 18, sun isa birnin Accran Ghana, a jiya Litinin, kuma an shirya rabawa ga sauran kasashe 17 nan da 'yan kwanaki.

Kasashen da za su ci gajiyar kayayyakin sun hada da Ghana da Nijeriya da Senegal da Gabon da Saliyo da Guinea-Bissau da Togo da Benin da Cote d'Ivoire da Gambia da Mali da Liberia da Guinea da Burkina Faso da Jamhuriyar Congo da Equatorial Guinea da Cape Verde da Sao Tome and Principe.

Kayayyakin bukatun gaggawa da ceton rayuka da aka tura cikin jirgin dakon kaya da Sin ta yi shata sun hada da kayayyakin kare kai da marufin baki da hanci nau'in N95 da rigunan kariya da safar hannu da tabarau da na'urorin taimakon numfashi da na auna zafin jiki.

Jakadan kasar Sin a Ghana Wang Shiting, ya ce duk da kasar Sin ta fara farfadowa daga annobar COVID-19 da karancin kayayyakin kiwon lafiya, abu ne mai muhimmanci ta taimakawa kawayenta dake Afrika don shawo kan cutar.

A nata bangaren, ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, wadda ta karbi kayayyakin a madadin kasashen 18, ta bayyana godiya matuka ga gwamnati da al'ummar kasar Sin, tana mai cewa, Sin ta nuna cewa lallai ita aminiya ce ta kwarai ga nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China