Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da sabbin mutane 32 sun shigo da COVID-19 Sin daga ketare
2020-04-07 13:08:18        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, jiya Litinin, an tabbatar da sabbin mutane 32 da suka kamu da cutar COVID 19 a kasar, duk sun shigo da cutar ce daga ketare, haka kuma babu wanda ya rasu sakamakon cutar a wannan rana, akwai kuma sabbin mutane 12 da ake zaton sun kamu da cutar, duk sun shigo ne daga ketare.

Ya zuwa karfe 12 na daren jiya, gaba daya yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar Sin ya kai 81740, kana yawan mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ya kai 89 a halin yanzu. Kuma yawan mutane da suka warke daga cutar ya kai 77167, yawan mamata ya kai 3331, sannan kuma yawan mutanen da ake sa ido kansu domin suka yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar ya kai 14499.

Dadin dadawa, a wannan rana, yawan mutanen da suka kamu da cutar ba tare da nuna alama ba ya kai 30, daga cikinsu 9 sun shigo ne daga ketare.

Kazalika, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a yankin Hong Kong da Macao da kuma Taiwan ya kai 1331. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China