Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dage haramcin tafiye – tafiye a Wuhan, bayan birnin ya shafe watanni a rufe
2020-04-08 10:17:33        cri

An dage haramcin tafiye-tafiye a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar Sin a yau Laraba, bayan ya shafe kusan makonni 11 a rufe, da nufin takaita yaduwar cutar COVID-19, inda motoci da jiragen kasa da sama na fasinjoji suka shirya barin birnin.

Kididdigar 'yan sanda masu kula da harkar sufuri a birnin Wuhan, ta yi hasashen cewa, yawan ababen hawa masu fita daga birnin a yau zai kai matsayin koli.

Yayin da karin kamfanoni suka koma aiki, an samu karuwar zirga-zirgar ababen hawa a Wuhan da kusan 400,000 cikin rabin wata da ya gabata, kuma ana sa ran daga yau Laraba, adadin zai zarce miliyan 1.8.

Har ila yau, ana sa ran sama da fasinjoji 55,000 za su bar Wuhan ta jirgin kasa a yau Laraba. Jimilar jiragen kasa masu dauke da fasinjoji 276 ne za su bar Wuhan zuwa biranen Shanghai da Shenzhen da sauran wasu birane.

Hukumomin kula da sufurin jiragen kasa sun bukaci fasinjoji su rika bari ana duba lafiyarsu lokacin shiga tasoshi, sannan su rika sanya marufin hanci da baki domin rage hadarin kamuwa da cuta.

Ma'aikata sun yi feshin magani a cikin jiragen kasa da hanyoyin shiga da fita da dakunan jira kafin a bude tasoshin.

Da safiyar yau Laraba ne filin jirgin saman Tianhe na Wuhan ya dawo da aikin zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida. Ana sa ran samun jigilar jiragen sama, sama da 200 a filin jirgin a wannan rana.

A ranar 23 ga watan Janairu ne aka ayyana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a Wuhan, ciki har da motocin haya na birnin da jirgen sama da na kasa, a wani yunkuri na dakile yaduwar annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China