Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya wajen samun nasarar shawo kan COVID-19
2020-04-07 21:02:39        cri

Yau Talata 7 ga wata, a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya, wajen samun nasarar shawo kan mummunar annobar cutar numfashi ta COVID-19.

A ranar 2 ga wata, a yayin babban taron MDD an zartas da shirin dokar "yaki da annobar COVID-19 cikin hadin gwiwar kasa da kasa" da kasashe 6, ciki har da kasashen Singapore da Ghana da Indonesiya suka gabatar da daftarin dokar. Gaba daya kasashe 188 ciki har da kasar Sin sun goyi bayan gabatar da daftarin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China