Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba sun bayar da karin tallafin yakar COVID-19 ga Afrika
2020-04-08 09:56:34        cri

A karo na biyu gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba sun bayar da tallafin yaki da cutar COVID-19 ga kasashen Afrika.

Tallafin dai ya kunshi kayayyakin kiwon lafiya wadanda aka raba ga kasashe 54 a Afrika yayin da nahiyar ke fuskantar karuwar yawan mutanen dake kamuwa da cutar.

A wannan karon kayayyakin lafiyar sun hada da na'urar taimakawa numfashi guda 500, da rigunan ba da kariya da gilashin rufe fuska 200,000, da na'urar gwajin zafin jiki 2,000, sai sauran kayayyakin gwaje gwajen lafiya kimanin 500,000 kamar yadda gidauniyar Jack Ma da Alibaba suka sanar ranar Litinin.

A watan Maris, gidauniyoyin biyu suka sanar da ba da tallafin takunkumin rufe fuska 100,000, da kayayyakin gwaje gwajen lafiya 20,000, da kuma rigunan ba da kariya 1,000 ga ko wace kasa cikin kasashen Afrika 54.

Baya ga tallafin kayayyakin kiwon lafiyar daga gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba, haka zalika gidauniyoyin biyu suna tsara tarukan musayar kwarewa tsakanin kwararrun masana kiwon lafiya na kasashen Afrika da Sin da sauran kasashen duniya domin yin musaya da hadin gwiwa ta hanyar intanet game da matakan kandagarki da kuma yaki da cutar ta COVID-19.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China