Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afirka ya kai sama da dubu 10
2020-04-08 12:46:05        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afirka ta fidda sabon rahoto dake cewa, ya zuwa ranar 7 ga wata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai 10075 a nahiyar, yayin da mutane 487 sun rasu sanadiyyar annobar, kuma gaba daya akwai mutane 913 da suka warke daga cutar. A halin yanzu, kasashe 52 na nahiyar Afirka suna fama da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Kana, wasu masana suna ganin cewa, saboda karancin karfin yin bincike, hakikanin adadin mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar Afirka ya fi alkulaman da aka samu.

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, masanan kasar Sin, da tawagogin likitoci masu ba da taimako ga kasashen Afirka, da kamfanonin kasar Sin da dama suna yin hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyoyi daban daban domin yaki da annobar, lamarin da ya nuna dunkulewar kasashen Sin da Afirka.

Yanzu, akwai likitocin kasar Sin kimanin dubu 1 dake aiki a kasashen Afirka, inda suke ba da goyon baya ga kasashen wajen kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ya zuwa yanzu, sun riga sun gudanar da ayyukan horaswa kan ilmin kiwon lafiya sama da 250, inda suka ba da horo ga mutane sama da dubu 10.

Haka kuma, kasar Sin ta kafa tawagogin masana masu ba da shawara, domin yin mu'amala da likitocin kasashen Afirka 54 ta kafar bidiyo.

Ban da haka kuma, a ranar 6 ga wata, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar ga kasashen Afirka guda 18 sun sauka a kasar Ghana. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China