Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan majalissar wakilan Najeriya sun amince da bayar da albashinsu domin yaki da cutar COVID-19
2020-04-01 14:38:25        cri
'Yan majalisar wakilan tarayyar Najeriya su 360, sun amince da bayar da albashinsu na watanni 2, a matsayin gudummawarsu domin yaki da cutar COVID-19.

Kakakin majalisar wakilan Femi Gbajabiamila, ya ce gudummawar tasu za ta taimaka wajen samar da kayayyakin bukata ga jami'an lafiya dake kan gaba, a yaki da wannan annoba a yanayin da ake ciki.

Yanzu haka dai daukacin ministocin kasar 43, da attajiran kasar, da kungiyoyi, da bankuna, na ci gaba da bayar da tallafinsu na biliyoyin nairori, domin agazawa yakin da kasar ke yi da cutar ta COVID-19 a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China