Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu dauke da COVID-19 a Afirka ya haura mutum 10,000
2020-04-07 19:54:32        cri
Cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka ko "Africa CDC, ta ce ya zuwa Talatar nan, adadin masu dauke da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar ya kai mutum 10,075, yayin da cutar ta hallaka mutane 487.

"Africa CDC" dake karkashin kungiyar AU mai mambobin Afirka 55, ta bayyana wadannan alkaluma ne a Talatar nan, inda ta ce tuni cutar ta bulla a kasashen nahiyar 52.

Cibiyar ta kara da cewa, kawo yanzu, akwai mutane 913 da suka warke daga wannan cuta bayan kamuwa da ita. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China