Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na iya koyi da dabarun Sin na shawo kan COVID-19 in ji wani masani
2020-04-01 11:21:49        cri
Shugaban cibiyar samar da horo ta iBass dake birnin Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya Mohammed Abass, ya ce Najeriya na iya koyi da fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su, wajen shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 a cikin kasar dake yammacin Afirka.

Mohammed Abass ya bayyana hakan ne, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yana mai cewa, akwai matukar bukatar daukar matakan dakile ci gaba da bazuwar annobar zuwa sauran sassan al'ummar kasar ta hanyar ilmantarwa.

Ya ce kamata ya yi Najeriya ta yi duba, ga irin dabarun da Sin ta aiwatar, na dakatar da bazuwar annobar, ta kuma goyi bayan managartan shirye shirye, na tunkarar kalubalen lafiya da duniya ke fuskanta.

Abass ya kara da cewa, darasin da za a iya koya yayin da ake yaki da wannan annoba, shi ne bukatar kyautata tsarin kiwon lafiya mai nagarta a dukkanin sassan kasa. Ya kuma ce kamata ya yi mahukuntan kasar su fadada ilmantar da al'umma game da cutar, musamman ma kan batutuwa masu daure kai masu nasaba da ita, domin rage bazuwar ta a mataki na al'ummu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China