Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cote d'Ivoire ta samu rahoton farko na wanda cutar COVID-19 ta hallaka
2020-03-30 13:39:52        cri
A ranar Lahadi kasar Cote d'Ivoire ta bayar da rahoton mutum na farko da cutar numfashi ta COVID-19 ta kashe bayan da aka samu sabbin mutane 25 da suka kamu da cutar a kasar, wanda hakan shi ya kawo jimillar yawan mutanen da suka kamu da cutar ta COVID-19 kimanin 165 a kasar, kamar yadda ma'aikatar lafiya da tsaftar muhalli ta kasar ta sanar.

Ministan lafiyar kasar Cote d'Ivoire Eugene Aka Aouele, ya sanar da cewa, a ranar Lahadi ne aka samu mutum na farko da cutar COVID-19 ta kashe a kasar. An tabbatar da hakan ne bayan binciken da aka gudanar bayan mutuwar majinyacin.

Domin takaita bazuwar cutar a kasar, gwamnatin Cote d'Ivoire ta dauki matakai masu yawa, da suka hada da hana zirga-zirga tsakanin birnin Abidjan da sauran biranen dake kewaye dashi, tun daga daren ranar Lahadi, kuma an haramtar shigar baki matafiya daga wasu kasashen waje cikin kasar, an rufe kan iyakokin shiga kasar ta sama da kasa da ta ruwa, kana an rufe dukkan makarantun ilmi, da gidanjen sayar da abinci da wuraren shakatawa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China