Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya na neman amincewar kashe dala biliyan 1.2 domin daga darajar sashen kiwon lafiya
2020-04-06 16:42:30        cri
Ministar ma'aikatar kudi ta tarayyar Najeriya Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin kasar na neman amincewar majalissar dokoki, game da wani kuduri da zai ba da damar samar da wani asusu, na dalar Amurka biliyan 1.2, kudaden da za a kashe su a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ta hanyar daga darajar kayayyakin kula da lafiya, da kuma baiwa jihohin kasar tallafin da suke bukata a wannan fanni.

Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne a daren Asabar, bayan ganawar ta da shugabancin majalissar dokokin kasar. Ta ce ana fatan tattara kudaden ne daga asusu daban daban na musamman na gwamnatin kasar, da kuma sauran kudade na bashi da tallafi da kasar ke fatan samu, daga sassan kasa da kasa.

A wani ci gaban kuma. Sudan ta kudu ta zamo kasar baya bayan nan, kuma ta 51 a nahiyar Afirka, wadda ta samu bullar cutar COVID-19. An tabbatar da kamuwar mutum na farko a kasar ne a jiya Lahadi. Hakan dai na nuna cewa, kasashen Comoros, da Lesotho da Sao Tome da Principe ne kadai cutar ba ta bulla ba, a daukacin nahiyar ta Afirka.

Bisa alkaluman da cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka ta fitar a jiya Lahadi, kawo yanzu, jimillar masu dauke da cutar a nahiyar ya kai mutum 8,736, tuni kuma ta hallaka mutane 399.

Sakamakon bullar cutar a sassan nahiyar Afirka daban daban, kasashen nahiyar da dama na ci gaba da tsawaita lokutan dakatar da cudanyar al'umma, tare kuma da laluben hanyoyin samar da kudaden da ake bukata, domin yaki da wannan cuta. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China