Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 5,255
2020-04-01 10:34:11        cri

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afrika wato Africa CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 172, yayin da wadanda aka tabbatar sun kamu ya zarce 5,255, ya zuwa jiya Talata.

Cikin rahotonta na baya-bayan nan, cibiyar Africa CDC, ta ce an samu barkewar cutar a kasashen nahiyar 47.

Har ila yau, cibiyar ta bayyana cewa, kasashen da cutar ta fi kamari sun hada da Africa ta Kudu mai mutane 1,326 da suka harbu, sai Masar mai mutane 656 da kuma Algeria mai mutane 582 da suka harbu.

Ta kara da cewa, akwai kuma wasu mutane 371 da suka warke daga cutar a fadin nahiyar.

La'akari da yadda cutar ke bazuwa a fadin nahiyar, alkaluman cibiyar sun nuna cewa, an samu sama da sabbin mutane 384 da aka tabbatar sun kamu da cutar bayan rahoton da ta fitar a ranar Litinin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China