Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WIPO: Sin ta gabatar da neman hakkin mallakar fasaha mafi yawa a shekarar 2019
2020-04-08 10:57:50        cri
Jiya Talata, kungiyar kare ikon mallakar ilmi ta kasa da kasa wato WIPO ta bayyana cewa, a shekarar 2019, kasar Sin ta sha gaban Amurka, wadda ta gabatar da neman hakkin mallakar fasaha mafi yawa bisa tsarin yarjejeniyar hadin gwiwar mallakar fasaha ta PCT na kungiyar.

Bisa rahoton da kungiyar WIPO ta fidda, a shekarar 2019, kasar Sin ta gabatar da bukatar hakkin mallakar fasaha guda 58990 bisa tsarin PCT, wadda ta wuce adadin da kasar Amurka ta gabatar, wato 57840, lamarin da ya sa, kasar Sin ta zama kasar da ta fi amfani da tsarin. Haka kuma, babban daraktan kungiyar WIPO Francis Gurry ya bayyana cewa, a shekarar 1999, kungiyar ta sami bukatar hakkin mallakar fasaha guda 276 daga kasar Sin, sa'an nan, a shekarar 2019, adadin ya karu zuwa 58990, wanda ya ninka har sau 200 cikin shekaru 20.

Ya ce, yanzu kasar Sin ta kai matsayi na farko bisa adadin neman mallakar fasaha da ta gabatar, lamarin da ya nuna cewa, a halin yanzu, kasashen Asiya sun fi mai da hankali wajen yin kirkire-kirkire, har bukatar hakkin mallakar fasaha da kungiyar ta samu daga kasashen Asiya ya kai sama da rabin wanda kungiyar ta samu bisa tsarin PCT. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China