Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WIPO: Yawan rokon mallakar fasaha da Sin ta yi ya kai kusan kaso 50 bisa na duk duniya a bara
2019-10-17 11:09:01        cri
Hukumar dake sa ido kan ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa wato WIPO a takaice a jiya Laraba ta bayar da rahoton na shekara-shekara game da ma'aunin ikon mallakar fasaha na kasa da kasa (WIPI), inda aka nuna cewa, a shekarar 2018, masu yin kirkire-kirkire na duk duniya sun samar da rokon mallakar fasaha har miliyan 3.3, hakan ya tabbatar da samun karuwa cikin shekaru 9 da suka wuce a jere. Ciki kuwa, yawan rokon da aka gabatar daga kasar Sin ya kai kusan kaso 50% bisa na duk duniya.

Hukumar WIPO dake da hedkwatarta a Genevan kasar Switzerland ta bayyana wannan sakamako ne bisa rahoton da ta gabatar a wannan rana.

Rahoton ya kuma nuna cewa, matsayin Asiya na yanki mafi samu yawan rokon mallakar fasaha a duniya ya samu ingantuwa. A shekarar 2018, yawan rokon mallakar fasaha da aka gabatarwa hukumomin daban daban dake kula da aikin na Asiya ya kai kaso 66.8, ya karu sosai idan aka kwatanta da na kaso 50.8 a shekarar 2008. Baya ga haka, hukumar WIPO ta nuna cewa, an yi haka ne sakamakon ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China