Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude kasaitaccen bikin baje kolin fasahohi zamani na kasar Sin a Shenzhen
2019-11-14 10:50:08        cri

Yan kasuwa da masu zuba jari daga kasashe da shiyyoyin duniya sama da 100 a ranar Laraba sun halarci bikin baje kolin manyan fasahohin zamani na kasar Sin (CHTF), karo 21, wanda aka gudanar a birnin fasahar zamanin kasar Sin dake Shenzhen a kudanecin kasar Sin.

Bikin mai taken farfado da babban yankin Greater Bay ta hanyar bude kofa da kirkire-kirekire, sama da ayyuka 250 za'a gudanar a yayin bikin. Sabbin kayayyakin kirar fasahohin zamani, da suka hada da sabbin kayayyakin fasahohin zamani masu tsimin makamashi, da fasahohin kare muhalli, na'urorin latironi na zamani, da na'urorin samar da bayanai a birane, da na fannin fasahohin jiragen sama ake baje kolinsu a bikin na kwanaki biyar.

Manyan kamfanonin fasahar zamani na kasar Sin Huawei, ZTE da wasu kamfanonin kasar Sin masu yawa dake cikin jerin sunayen manyan kamfanoninn kirkire-kirekire na fasahohin Shanghai (STAR market), da suka hada da Arcsoft da Cambricon sun shiga baje kolin.

Gwamnatin birnin Shenzhen ta kaddamar da baje kolin na CHTF a karon farko ne a shekarar 1999 da nufin bunkasa ci gaban tattalin arziki ta hanyar fasahohin kirkire-kirkire, kuma tun daga wancan lokacin ake ci gaba da gudanar da bikin baje kolin a duk shekara. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China