Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a zurfafa alaka a fannin kimiyya da fasahar kere-kere
2019-11-04 09:30:31        cri

Shugaban kungiyar kimiyya da fasahar kere-kere ta kasar Sin Wan Gang, ya bayyana kudurin kasarsa na raya kimiyya da fasahar kere-kere da karfafa tsarin tafyar da harkokin kasa da kasa.

Wan Gang ya bayyana hakan ne, yayin taron dandalin raya kimiyya da fasahar kere-kere da tafiyar da harkokin kasa da kasa. Yana mai cewa, fasahar kere-kere da dunkulewar tattalin arzikin duniya, sun karfafa kyakkyawar amfani da albarkatu.

Jami'in na kasar Sin ya ce, kamata ya yi kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasahar kere-kere, su kasance a sahun gaba wajen zurfafa bude kofa da karfafa alaka tsakanin kasashen duniya, ta yadda za a kawar da illolin rashin dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Bugu da kari, ya nanata cewa, kasar Sin za ta zurfafa alaka da tsarin jagoranci a bangaren kimiyya da fasahar kere-kere, da karfafa kirkire-kirkire da bunkasa ilimin kimiyya.

A nasa jawabin, tsohon gwamnan babban bankin kasar Sin Zhou Xiaochuan, ya yi gargadin cewa, yadda ake yayata fasahar kwaikayon tunanin dan-Adam(AI), gibin kudin shiga da jama'a ke samu na iya karuwa, akwai kuma yiwuwar mutum-mutumin dan-adam na iya maye gurbin wasu kananan ayyuka da jama'a ke yi, musamman, yadda aka hade wannan fasaha da muhimman bayanai da sadarwa waje guda.

A don haka, ya bukaci a kara zage damtse wajen rage tasirin da sabbin fasahohi kere-kere ke yi kan guraben ayyukan yi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China