Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamian kasashe daban-daban sun koyi dabara daga ajin jirgin kasa mai saurin tafiya da Sin ta gabatar
2019-10-23 10:07:49        cri

 

An gudanar da ajin koyar da ilmin sadarwar layin dogo ga kasashe masu tasowa na bana a jiya Talata a kwalejin koyon sana'ar gudanar da layin dogo na Liuzhou na jihar Guangxi. Jami'ai 23 daga kasashen Mauritius, Panama, Uzbekistan, Nijeriya, Azerbaijan da Kenya da dai sauransu ne suka ziyarci kwalejin don ganewa idonsu yadda ake gudanar da aiki a tashar jiragen kasa masu saurin tafiya da koyon dabaru da fasahohi. Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ce ta dauki bakuncin wannan aiki, kuma jami'ar koyon ilimin zirga-zirga na Kudu Maso Yammacin kasar Sin da kwalejin ba da ilmi ga jami'an kasuwanci na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ne suka gabatar da wannan aji cikin hadin kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China