Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da annobar cutar COVID-19 a Rwanda ya kai 50
2020-03-27 11:06:48        cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Rwanda, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis cewa, yawan wadanda suka kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ya kai 50 daga mutane 41 a baya.

Sanarwar ta ce, sabbin marasa lafiya guda 9 da aka gwada suna dauke da cutar, sun hada da matafiya guda biyar daga hadaddiyar daular Larabawa sai kuma mutum guda daga Amurka, an kuma killace su da isowarsu.

Sauran mutanen uku, sun yi mu'amala ne da matafiyan da aka tabbatar sun kamu da cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China