Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya haramta zirga-zirga a jihohin Lagos da Ogun da birnin Abuja, na tsawon kwanaki 14
2020-03-30 10:29:10        cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin dakatar da zirga-zirga a jihohin Lagos da Ogun da birnin tarayya Abuja, na tsawon kwanaki 14, daga karfe 11 na daren yau Litinin, a wani bangare na dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

Shugaban ya bada umarnin ne a jiya, cikin jawabin da ya gabatar, karon farko bayan bullar cutar a kasar.

Muhammadu Buhari, ya bukaci dukkan mazauna yankunan su zauna a gida, sannan a dage duk wata zirga-zirga tsakanin jihohin kasar. Haka zalika, ya nemi a dakatar da dukkan harkokin kasuwanci a wadancan yankuna na tsawon lokacin.

A cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, an samu sabbin mutane 14 da suka kamu da cutar a kasar, inda aka samu 9 a jihar Lagos da 5 a birnin Abuja. Ya zuwa karfe 9:30 na daren jiya, mutane 111 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, inda mutum guda ya mutu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China