Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu cutar COVID-19 a Afrika ta kudu ya karu zuwa 927
2020-03-27 12:04:20        cri
Ministan lafiya na kasar Afrika ta kudu, Zweli Mkhize, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya karu da 218, zuwa 927, a kan yadda ya kasance a ranar da ta gabata.

Adadin na jiya, shi ne mafi yawa da aka samu a rana guda, tun bayan barkewar cutar a kasar a ranar 5 ga wata.

Cutar ta fi kamari a Lardin Gauteng dake da mutane 409 da suka kamu, sai Western Cape dake bi masa baya da mutane 229, sai kuma KwaZulu-Natal, dake da masu dauke da cutar 134. Dukkan sauran lardunan kasar 6, sun bada rahoton samun wadanda suka harbu da cutar.

Har ila yau, a jiya Alhamis, Shugaban kasar, Cyril Ramaphosa, ya yi gargadin adadin masu cutar a kasar ka iya karuwa fiye da haka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China