Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta Kudu: kasashen G20 za su hada hannu wajen magance tasirin COVID-19
2020-03-27 10:59:39        cri
Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce kasashen G20 sun amince su bullo da wata ingantacciyar hanyar magance tasirin cutar COVID-19, kan harkokin tattalin arziki da zamantakewa.

Cyril Ramaphosa ya bayyana haka ne a jiya, bayan taron da suka yi na shugabannin kasashen G20, dangane da cutar COVID-19.

Ya ce yana ganin za a aiwatar da matakan da aka dauka nan bada jimawa ba. Inda ya ce akwai bukatar a yaki cutar tare da ceton rayukan jama'a da tallafawa kasashen dake cikin mawuyacin hali da kuma sanya bukatun nahiyar Afrika a kan gaba. Ya ce a matsayinsu na nahiyar Afrika, sun yi kira ga Kasashen G20 su taimaka musu, ta yadda kasashen nahiyar za su mayar da hankali wajen yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China