Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Larabawa sun amfana da dabarun Sin na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19
2020-03-27 09:51:55        cri
Kwararrun masana da suka halarci taro ta kafar bidiyo a ranar Alhamis sun bayyana cewa, dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 sun kasance babban abin koyi ga kasashen Larabawa, a kokarin da suke na yaki da annobar.

Taron bidiyon game da matakan yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 na hadin gwiwa ne tsakanin jami'an lafiya da kwararrun kasar Sin da na kasashen duniya sama da 10 daga yammacin Asiya da arewacin Afrika, da suka hada da Falastinu, Lebanon, Sudan da Kuwait.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China