Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yabawa taimakon da kasar Sin ke bayarwa wajen yaki da COVID-19 a nahiyar Afrika
2020-03-23 10:20:22        cri

Manyan jami'an gwamnatin Habasha da na sauran kasashen Afrika da hukumomi, sun yabawa taimakon da kasar Sin ke ba nahiyar a yakin da ake da annobar COVID-19.

Kasar Sin, wadda ita ma take yaki da cutar a cikin gida, ta na samun yabo a fadin nahiyar Afrika, saboda goyon baya da taimakon da take ba kasashen nahiyar da hukumomin yankunan nahiyar, a yaki da annobar.

A wani bangare na taimakon da kasar Sin ke ba nahiyar Afrika wajen dakile yaduwar cutar, kwararru da jami'an lafiya da na kwastam na kasar, sun gabatar da bayanai game da yadda suka fuskanci cutar COVID-19 a wani taro da aka yi ta bidiyo da jami'ai da kwararrun kan kiwon lafiya daga cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC da na wasu kasashen nahiyar 24, lamarin da ya nuna kudurin kasar Sin na bayar da bayanai da taimakon nahiyar a yaki da annobar.

Da take tattaunawa da Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministar lafiya ta Habasha, Lia Tadesse, ta jaddada irin goyon bayan da Sin ke ba kasar ta gabashin Afrika da sauran kasashen nahiyar a yakin da suke da cutar, wanda ya hada da tallafin kayayyaki da bayanai da sauransu.

Kasar Sin ta bayar da kayayyakin gwaji ga kasashen Afrika ta hannun cibiyar CDC da kuma kayayyakin daukin gaggawa ga kasashen da cutar ta shafa, baya ga jami'anta na lafiya dake taimakawa a nahiyar.

Baya ga goyon bayan da gwamnatin Kasar Sin ke ba nahiyar Afrika a yaki da cutar, kamfanoni da kungiyoyin al'umma na kasar, su ma suna samar da kayayyakin gaggawa da ake bukata a kasashen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China