Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu dauke da cutar COVID-19 a Najeriya ya kai mutum 65
2020-03-27 21:01:30        cri
Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce ya zuwa daren jiya Alhamis, ta samu rahoton karuwar mutane 14 da suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan ya kai jimillar masu dauke da cutar 65. Cikin wannan adadi a cewar cibiyar, an sallami 3 daga asibiti bayan sun warke, yayin da kuma mutum guda ya rasu.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, NCDC ta ce an gano mutane 6 dauke da cutar a wani jirgin ruwa, kuma 3 daga cikin su matafiya ne da suka komo kasar daga ketare, kana daya daga cikin su ya yi cudanya ta kusa da wani wanda ya harbu da cutar.

Kawo yanzu dai akwai wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da aka tabbatar sun harbu da cutar, yayin da wasu kuma ke ci gaba da kebe kan su. Cikin wadanda aka tabbatar sun harbu, akwai gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Abba Kyari.

A daya bangaren kuma, gwajin da aka yiwa sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha, da ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire, da babban sakataren ma'aikatar Mashi Abdulaziz Mashi, ya nuna jami'an ba sa dauke da wannan cuta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China