Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin Najeriya sun sadaukar da rabin albashinsu don yakar COVID-19
2020-03-29 16:31:36        cri
Kimanin ministocin Najeriya 43 sun bayar da rabin albashinsu na watan Maris domin taimakawa gwamnatin kasar a matsayin gudunmowarsu don yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar.

A wata sanarwar da ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed ya fitar wanda aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, sun yanke wannan shawara ne a matsayin nuna goyon bayansu da tallafawa kokarin gwamnatin kasar na dakile annobar.

Ya kara da cewa, wannan cuta da ta barke ta zama annoba ga duniya baki daya, wacce ke bukatar dukkan bangarorin kasa da matakan nahiyoyi da kananan yankuna su hada kai don yin aiki tare domin ba da gudunmowarsu ta kudade da nuna goyon baya daga dukkan bangarorin al'umma da nufin kawar da cutar.

Haka zalika, wasu daga cikin manyan attajiran Najeriya, da kungiyoyi, da bankuna, tuni suka ba da gudunmowar biliyoyin Naira domin taimakawa yakin da ake da annobar ta COVID-19.

Daga cikinsu, akwai bankin UBA, wanda ya ba da gundumowar dala miliyan 14.

Wasu masu ruwa da tsaki na kamfanonin mai, karkashin jagorancin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, a ranar Juma'a sun sanar da ba da gudunmowar dala miliyan 30.

Ya zuwa daren Juma'a, an tabbatar da mutane 81 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Najeriya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China