Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 15 sanadiyyar fashewar bututun man fetur
2020-03-16 09:47:25        cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce an gano gawarwaki 15 a wajen da gobara ta auku, jiya Lahadi a yankin Abule Ado na jihar Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar.

Mukaddashin shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da adadin gawarwakin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9 na safiyar jiya Lahadi, agogon kasar. Ya ce wajen lamarin ya auku na kusa da kwalejin 'yan mata ta Bethlehem, inda sama da dalibai 60 na kwalejin suka ji raunika daban-daban, kuma tuni aka garzaya da su asibitin rundunar sojin ruwan kasar.

A cewarsa, daga bisani, gobarar da ta tashi, ta yadu zuwa bututun man kamfanin mai na kasar dake yankin, sai dai an kulle bututun a wani mataki na kandagarki.

A nasa bangaren, darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Lagos, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin gobarar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China