![]() |
|
2020-03-22 16:19:38 cri |
Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ya nuna cewa matakin zai fara aiki ne tun daga gobe Litinin.
Babban darakatn kula da hukumomin gudanarwar filayen jiragen saman Najeriya Musa Nuhu, ya fada cikin wata sanarwa cewa, bisa halin da ake ciki a yanzu lamarin ya shafi rufe filayen jiragen saman kasa da kasa na Murtala Muhammad dake birnin Ikko da na Nnamdi Azikwe dake Abuja, kuma an dakatar da duk wata zirga zirgar jiragen sama daga kasashen ketare zuwa Najeriyar in ban da sufurin gaggawa da mafiya muhimmanci.
To sai dai kuma, matakin bai shafi zirga zirgar jiragen sama na cikin gidan kasar ba.
Kawo yanzu, Najeriya ta samu wadanda suka kamu da cutar COVID-19 kimanin 22 a kasar, yayin da gwamnatin Najeriyar ke cigaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar, matakan sun hada da tsaurara matakan rufe dukkan iyakokin kasar.(Ahmad Inuwa Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China