Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nigeriya ta bayyana matakan Sin na yaki da COVID-19 a matsayin abun koyi
2020-03-14 16:31:50        cri
Darakta janar na cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya ce kasar Sin ta yi nasarar rage masu kamuwa da cutar COVID-19 ta hanyar hada hannu da dukkanin al'ummarta wajen tunkarar cutar.

Chikwe Ihekweazu, ya ce akwai bukatar kowa ya ba da gudunmuwa wajen dakile yaduwar cutar a kasar dake yammacin Afrika.

Jami'in wanda a yanzu haka ya killace kansa, bayan ziyarar da ya kawo kasar Sin, ya ce ya kamata al'ummar Nijeriya su bi irin hanyoyin da Sinawa suka bi, wajen taimakon gwamnati. Ya kara da cewa, akwai bukatar al'ummar kasar su taimaki gwamnati ta hanyar yayata sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa, ayyana cutar da aka yi a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya, na bukatar bayanai na gaskiya ba fargaba ba.

Har ila yau, Chikwe Ihekweazu, ya ce ya kamata gwamnatin kasar ta kara zage damtse wajen kara sa ido a tasoshin shiga kasar da kuma karfafawa mutane gwiwar killace kansu na tsawon kwanaki 14 idan sun dawo daga kasashen da aka tabbatar da barkewar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China