Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Lagos ta Nijeriya ta dauki karin matakan dakile yaduwar COVID-19
2020-03-24 10:19:48        cri

Hukumomi a jihar Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya, sun gabatar da karin matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 a jihar, ciki har da ba da umarnin zama a gida.

Kwamishinan kula da muhalli da albarkatun ruwa na jihar, Tunji Bello, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Lagos, ya ba 'yan bola jari umarnin barin duk wani wurin tara shara nan take, a matsayin wata hanya ta dakile yaduwar cutar a jihar.

Tunji Bello, ya kuma umarci hukumar kwashe shara ta jihar ta fara aiwatar da umarnin nan take.

Ya ce wannan yunkuri ya yi daidai da matakan da aka gabatar na dakile yaduwar cutar a jihar.

Baya ga haka, gwamnatin jihar ta bukaci masu yawon shakatawa su kauracewa wuraren shakatawa domin biyayya ga shawarar da aka bayar na kaucewa taron jama'a da ya haura mutane 50 a wuri guda.

Har ila yau, gwamnatin jihar ta ba ma'aikatanta dake matakin albashi na 01-12 su zauna a gida daga jiya Litinin.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya ba da umarnin, ya ce umarnin zama a gida, wani bangare ne na kara dakile yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China