Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna ta Trump ta wayar tarho
2020-03-27 15:37:30        cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa gayyatarsa.

Yayin zantawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata sassan lafiya da hana yaduwar cututtuka da masanan kasashen Sin da Amurka su rika tuntubar juna game da yanayin annoba a duniya da alakar kasashin biyu a fannin kandagarki da hana yaduwar cututtuka. Ya ce, a shirye kasar Sin take ta ci gaba da raba bayanai da fasahohinta ga Amurka ba tare da wata rufa-rufa ba. Wasu larduna, birane da kamfanonin a kasar Sin sun samar kayayyakin kiwon lafiya ga Amurka. Kasar Sin ta fahimci mawuyacin halin da Amurka take ciki, don haka, a shirye take ta taimaka mata gwargwadon karfinta. Shugaba Xi ya ce, yana fatan Amurka za ta dauki matakan da suka dace, wajen inganta alakar dake tsakanin kasashen biyu, bangarorin biyu, za su yi aiki tare, don karfafa alaka a fannoni kamar, jure annoba, raya alaka da babu tashin hankali, babu fito na fito, mutunta juna da cin moriya tare.

A nasa jawabin, Trump ya bayyana cewa, fasahohin kasar Sin abin koyi ne. Yana mai cewa, zai sanya ido shi da kansa, don tabbatar da cewa, Amurka da Sin, sun daina tsoma baki a harkokin juna, da mayar da hankali kan matakan da suke dauka kan alakar yaki da annoba. Ya ce, yana godiya da taimakon kayayyakin lafiya da kasar Sin ta samarwa kasarsa, a gabar da take yaki da wannan annoba, da karfafa musaya a fannin ma'aikata da kayayyakin kiwon lafiya, ciki har da hadin gwiwa a fannin samar da magungunan rigakafin annoba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China