Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya aike da sakon jaje ga sarkin kasar Sifaniya
2020-03-21 21:02:06        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako ga sarkin kasar Sifaniya King Felipe VI, a kwanakin baya, inda a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugaba Xi ya jajantawa gwamnati da jama'ar kasar Sifaniya, kan barkewar cutar COVID-19 a kasar cikin wadannan kwanaki.

Shugaban kasar Sin ya ce, kasarsa na goyon bayan kokarin kasar Sifaniya na neman dakile yaduwar cutar COVID-19, kana tana son bayyana fasahohinta a fannin kandagarkin cutar da jinyar majiyyata ga kasar Sifaniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China