Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muhimmancin al'umma ita ce ka'idar da Xi Jinping ya bi wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-18 21:26:09        cri

Cutar numfashi ta COVID-19 ita ce cutar da ta shafi lafiyar al'umma cikin gaggawa da ta yaduwa cikin sauri, wadda ta bazuwa a duk fadin kasar, da kuma mafi wahalar kandagarki da dakilewa, da kasar Sin ta gamu da ita tun bayan aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Bayan barkewar cutar, kwamitin tsakiyar JKS ya mai da hankali matuka kan dakile yaduwar cutar, kana, babban sakataren JKS Xi Jinping ya mai da hankali kan batun a ko da yaushe, inda ya mai da aikin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 aiki mafi muhimmanci, ya kuma jagoranci aikin yaki da cutar da kansa, lamarin da ya sa kaimi ga al'ummomin kasar wajen hada kai don yaki da cutar.

"Mun ba da muhimmanci ga tsaron rayuka da lafiyar al'ummomin kasar", "Ba wanda zai hana ci gaban al'ummar Sinawa da kasar Sin", wannan shi ne abin da al'umma suka sanya a gaba.

A kalli bidiyon din da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar mai taken "Muhimmancin al'umma—yadda Xi Jinping yake jagorantar aikin yaki da cutar COVID-19". (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China