Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya zanta da shugabannin Kazakhstan, Poland da Brazil
2020-03-25 10:30:59        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta daya bayan daya, da shugabannin kasashen Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev da na Poland, Andrzej Duda da na Brazil, Jair Bolsonaro ta wayar tarho, a jiya da daddare.

Yayin zantawarsa da shugaban kasar Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev, Xi Jinping ya ce, yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa da sauri, lamarin da ya kasance babban kalubale ga kasa da kasa. Ya ce Kasar Sin, makwabciya ce kuma abokiyar Kazakhstan bisa manyan tsare-tsare, kuma ta san halin da kasar Kazakhstan take ciki, yana mai cewa Sin za ta taimaka tare da goyon bayan kasar cikin himma da kwazo.

Sa'an nan, cikin zantawarsa da shugaban kasar Poland, Xi Jinping ya ce, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnati da al'ummomin kasar Poland sun nuna goyon baya ga kasar Sin, kuma al'ummomin Sin na godiya matuka. Ya ce bisa ra'ayin dunkulewar kasa da kasa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwarta da kasar Poland da ma sauran kasashen duniya wajen dakile yaduwar annobar, domin kiyaye lafiyar al'ummomin kasa da kasa.

Bugu da kari, cikin zantawarsa da shugaban kasar Brazil, Xi Jinping ya jinjina tare da bayyana goyon baya ga gwamnati da al'ummomin kasar Brazil kan yakin da suke da cutar numfashi ta COVID-19. A cewar Xi Jinping, kasar Sin na son taimakawa kasar Brazil kamar yadda take bukata, domin ba da gudummawa wajen dakile yaduwar cutar cikin kasashen duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China