Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana taimakawa aikin kandagarki da dakile cutar COVID-19 a duniya
2020-03-27 15:31:25        cri
A halin da ake ciki, cutar COVID-19 tana ci gaba da bazuwa a fadin duniya. A matsayinta na kwararriya wajen kandagarki da kuma dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta karade dukkannin kasashen duniya, ta ba da tallafin kayayyakin kiwon lafiya, da tura tawagar kwararrun likitoci don tallafawa yaki da annobar, ta kuma tura jami'an lafiya domin yin aiki tare da takwarorinsu na kasashe daban daban. Sin tana taimkawa kasashen da cutar tafi yin kamari.

A ranar 26 ga wata, kwamitin kula da harkokin lafiya na kasar Sin da jami'an lafiyar kasar Masar sun gudanar da taron kwararrun masana kiwon lafiya ta kafar bidiyo game da yadda za'a tinkari sabuwar annobar da ta barke. A lokacin taron ta kafar bidiyon, kwararrun kasar Sin sun yi musayar kwarewar da kasar ta Sin ke da shi wajen aikin dakile yaduwar annobar da suka hada da aikin kandagarki da dabarun dakile bazuwar cutar, gami da kula da mutanen da suka kamu da cutar, da yadda ake bibiyar sabbin hanyoyin da cutar ke yaduwa, kana sun yi musayar kwarewar tare da kwararrun kasar Masar domin ba su shawarwari game da yadda Masar za ta yi galaba a ayyukan yaki da cutar ta COVID-19.

A wannan rana, jami'ai da kwararru daga ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon, da wakilan hukumar lafiya ta duniya WHO dake Lebanon su ma sun shiga taron ta kafar bidiyo tare da kwararrun kasar Sin a fannin yaki da annobar domin samun ilmi kan kwarewar da kasar Sin ta samu a yaki da annobar. Baya ga jami'an lafiyar Lebanon, akwai kuma wasu karin jami'ai daga kasashen yammacin Asiya da arewacin Afrika, da suka hada da kasashen Syria, Sudan, Iraq, Kuwait da Qatar, su ma sun halarci taron musayar kwarewar.

Gwamnatin kasar Burundi ta fitar da wata sanarwa game da ayyukan kandagarki da dakile sabbin hanyoyin yaduwar cutar ta COVID-19 a ranar 25 ga wata, inda ta yabawa gwamnatin Sin bisa ga taimakon kayayyakin lafiyar da ta baiwa kasashen nahiyar Afrika wadanda suka hada da kasar Burundi. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China